Bayan Rigakafin Astrazeneca: Mutane 79 sun Kamu da Cutar Daskarewar Jini a ƙasar Burtaniya
A wani rahoto da ƙasar Burtaniya ta fitar ya nuna cewa kimanin mutum 79 sun kamu da cutar daskarewar jini bayan an musu rigakafin Astrazeneca a karon farko.
Shugaban hukumar MHRA ya ce daga lokacin da aka fara rigakafin zuwa ran 31 ga watan Maris an yiwa mutane 20 miliyan allurar rigakafin a karon farko.
Sai dai a Najeriya, hukumomi sun ce bayan sati ɗaya da fara yiwa yan ƙasa allurar rigakafin Astrazeneca, ba’a samu wata matsala ta daskarewar jini ba a faɗin ƙasar Aƙalla 79 sun kamu da cutar daskarewar jini a Burtaniya bayan anyi musu allurar rigakafin Astrazeneca.
Shugaban hukumar hukumar ƙayyade magunguna na Burtaniya (MHRA), June Raine, shine ya faɗi haka a wani taro da suka yi.
Read Also:
Shugaban MHRA ya bayyana cewa daga sanda ƙasar ta ƙaddamar da fara yin allurar rigakafin zuwa 31 ga watan Maris ɗin da ya gabata, an yiwa mutane 20 miliyan a karon farko.
Ya kuma ƙara da cewa, a wannan lokacin an samu waɗanda suka kamu da cutar daskarewar jini bayan an musu rigakafin su 79.
Daga cikin mutane 79 da suka kamu da daskarewar jinin, 19 daga cikin run riga mu gidan gaskiya.
A satin nan ne dai kwamitin yaƙi da cutar COVID19 ta ƙasar mu Najeriya ya bayyana cewa bayan mako ɗaya da fara rigakafin cutar ta Astrazeneca, ba’a samu wanda ya kamu da daskarewar jini ba.
Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana cewa ya zuwa yanzun an yiwa yan Najeiya 964,387 rigakafin ta Astrazeneca.
Ya ce gwamnatin tarayya na son a cikin shekaru biyu masu zuwa, ta yi wa yan Najeriya 70% rigakafin kafin ƙarewar shekarar 2022.