ASUU: Kungiyar na Barazanar Shiga Sabon Yajin Aiki

 

Wata takaddama ta masana’antu tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya na iya faruwa idan har ba a biya bukatun malaman ba.

Kungiyar ta fitar da sanarwa inda ta bayyana dalilin da zai sa a daura alhakin yajin aikin da suke barazanar zuwa a kan babban akawun tarayya, Ahmed Idris.

Kwanaki ASUU ta samu rashin fahimtar juna da gwamnatin tarayya game da Hadadden tsarin biyan albashin Ma’aikata.

Malaman jami’o’in gwamnati a duk fadin kasar suna barazanar shiga wani sabon yajin aiki.

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi wannan barazanar a lokacin da ta zargi Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris da kin biyan albashi da kuma fitar da kudaden alawus na sama da ma’aikata 1000 na tsawon watanni 13, jaridar The Nation ta ruwaito.

Lazarus Maigoro, shugaban ASUU na jami’ar Jos, ya yi wannan barazanar a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Jos, babban birnin jahar Filato.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa kungiyar ta zargi babban akanta da rura wutar rikici tsakanin gwamnatin tarayya da malaman.

ASUU ta ce:

“Duk da umarnin da shugaban kasar ya bayar na biyan albashin dukkan malaman jami’ar, AGF ya ki biyan albashinsu da suka fara daga watanni hudu zuwa 13.

“Babban abin damuwa shi ne yadda yayin da AGF ke kin biyan wadannan albashin, ma’aikatansa a cikin OAGF sun dukufa wajen kiran malaman da abin ya shafa da kuma dagewa kan cewa sai sun yi rajista da IPPIS kafin a biya su; wasu ma ana neman su hakura da wani bangare na albashinsu domin a biya su. Don haka a fili yake cewa wannan wani aiki ne da gangan daga AGF da mukarrabansa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here