Yajin Aikin: Bamu Samu Wata Sanarwa Daga Gwamnatin Kasa ba Kan Zama da Ministan Kwadago – ASUU
Shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU a Najeriya ya ce basu samu wata sanarwa daga gwamnatin kasar ba kan zama da ministan Kwadago, da nufin kawo karshen yajin aikin da suke yi.
Read Also:
Shugaban kungiyar Farfesa Emmanuel Osodeke ya fada wa sashen Pidgin na BBC cewa Ministan Kwadagon Chirs Ngige ne ma ya yi watsi da tattaunawar, ya kuma dakatar musu da albashi da tunanin cewa hakan zai sa su sauya matsayarsu.
A jiya Laraba ne Mista Ngige ya shaida wa manema labarai cewa za su yi wani zama da wakilan ASUU yau Alhamis da nufin kawo karshen tirka-tirkar da ke tsakaninsu, don ganin cewa dalibai sun koma azuzuwansu.
An shafe watanni daliban na zaune a gida, bayan gaza cimma matsaya tsakanin kungiyar malaman jami’o’in da gwamnatin Najeriya.