Atiku Abubakar ya yi Juyayin Rashin Sanata Ibrahim Mantu

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya waiwaya daga tun lokacin da Najeriya ke barin mulkin soja zuwa gwamnatin dimokuradiyya.

Atiku ya tuno farkon mulkin dimokuradiyya a Najeriya yayin da yake juyayin mutuwar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Nasiru Mantu.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya lura cewa marigayi tsohon dan majalisar yana daya daga cikin wadanda suka yi aiki don tabbatar da zaman lafiyar kasar a jamhuriya ta hudu.

Mutuwar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ibrahim Nasiru Mantu, ya haifar da bakin ciki ga ‘yan Najeriya da yawa, musamman ma daga bangarorin siyasa.

Daya daga cikin fitattun ‘yan kasar da ya nuna tsananin dacin rai da bakin ciki shine Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, wanda ya kadu kan rasuwar Mantu, PM News ta ruwaito.

Atiku a ranar Talata, 17 ga watan Agusta, ya tuna alakarsa da tsohon sanatan a lokacin da yake cikin rushasshiyar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) lokacin ya kasance babban ginshikin siyasa a babban Jam’iyyar Nigeria Republican Convention (NRC).

A cewar tsohon dan takarar shugaban kasar, Mantu ya yi aiki tare da wasu ‘yan siyasa don daidaita dimokradiyya mai tasowa a farkon mulkin Jamhuriya ta hudu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya ce:

“Mantu ya kasance mai matuƙar mahimmanci a wajen gudanar da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki a cikin waɗannan mawuyacin shekarun na koyon tsarin dimokuraɗiyya.”

Ya nuna jajircewar Mantu a matsayin ɗaya daga cikin halayen da ba a saba gani ba waɗanda suka gina shi tun daga kasa har zuwa matsayin babban jigo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here