Rigakafin Korona: Atiku Abubakar ya Zama na Farko a Nageriya da ya Karbi Allurar

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi allurar rigakafin cutar COVID-19.

Ana ganin cewa shine dan Najeriya na farko da ya karbi rigakafin.

The Cable ta ruwaito mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyana hakan ranar Alhamis. Atiku ya yi nasa alluran ne a Dubai, hadaddiyar daular larabawa.

“Muhimmancin rigakafin COVID-19 wajen dakile illar coronavirus abune wanda ba zamu gaji da jaddadawa ba, musamman a Afrika da Najeriya,” mai magana da yawun Atiku ya bayyana.

“Jiya (Laraba) ya na cikin wadanda aka yiwa rigakafi, Atiku Abubakar ya karbi rigakafin Pfizer/Biontech.”

“Ya kosa ya ga lokacin da yan Najeriya, musamman Likitoci masu faggen daga su fara karban nasu rigakafin.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here