Daga Karshe, Atiku ya Zaɓi Okowa a Matsayin Abokin Tafiyarsa
‘Dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana Gwamna Ifeanyi Okowa matsayin abokin tafiyarsa.
Duk da kwamitin shawari ta zabi Gwamna Wike na jihar Ribas, an gano cewa Atiku ya sakankance cewa Wike bayan kaunarsa.
Har ila yau, wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP, ba su aminta da Gwamna Wike ba ganin irin kusancin da kujerar take da ta shugaban kasa.
FCT, Abuja – Atiku Abubakar, ‘dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP, ya zabi Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai gabatowa.
Kwamitin gudanar da ayyuka na jam’iyyar PDP a ranar Laraba ya zabi Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, a matsayin wanda zai kasance mataimakin ‘dan takarar shugabancin kasan.
Read Also:
Mambobin NWC sun yi zabe inda Wike ya samu kuri’u 13 yayin da Okowa ya samu uku kacal, lamarin da yasa masu ruwa da tsakin suka aminta da Wike.
Sai dai, Atiku Abubkar na gano ya kasa sakin jiki da Wike a matsayin abokin tafiyarsa sabodaya sakankance cewa gwamnan baya kaunarsa.
Wike yayi wa Aminu Waziri Tambuwal aiki a zaben fidda gwani na 2019, duk da kuwa cewa Atiku ya zo ya lashe zaben, Arise Tv ta ruwaito.
Wasu manya a PDP an gano ba su aminta da Wike ba saboda tsananin kusancin mataimakin shugaban kasa da kujerar shugabancin kasan.
Ya sanar da zabinsa ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam’iyyar PDP ta lasa dake Abuja. Ya ce ya yanke wannan shawarar ne bayan dogon nazari da tattaunawa da masu ruwa da tsakin jam’iyyar.
A cewarsa, hukunci ne mai tsauri gare shi wurin yankewa duba da irin nagartattun mutanen da aka shawarcesa ya zaba daga ciki. “Ina farin cikin sanar da sunan Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin ‘dan takarar shugaban kasa.
Ina hango tafiyar da kasar mu, tare da dukkan ‘yan Najeriya da kuma gina zaman lafiya, hadin kai da cigaba ga kowa,” ya wallafa a shafinsa na Twitter.