Atiku Abubakar ya Koma Makaranta

 

Biyo bayan jita-jitan cewa Atiku ya koma Dubai da zama, dan siyasan ya yi martani.

Tsohon mataimakin shugaban kasan yace makaranta ya koma karo ilimi.

Ya ce Obasanjo ne ya bashi shawaran komawa makaranta.

Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran kujeran shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin da yasa ya dade ba ya Najeriya.

Rahotanni sun yadu cewa tsohon mataimakin shugaban kasan ya arce daga Najeriya tun bayan da ya sha kashi a zaben shugaban kasa a 2019.

Atiku ya bayyana cewa ya koma karatun digirinsa na biyu ne kan ilmin alaka tsakanin kasashe a jami’ar Cambridge dake kasar Birtaniya.

Atiku ya bayyana hakan ne bayan zaman majalisar dattawan jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP, ranar Alhamis, a Wadata Plaza, birnin tarayya Abuja, rahoton TheCable.

Yace:

“Mutane da yawa na tambayan cewa ina naje tun Satumba, kuma abin ya fara haifar jita-jita tsakanin mutane.”

“Ina mai cewa na koma makaranta ne domin karasa lakca a Mayu, saboda ina karatun digiri na biyu a Alakokin kasashe a jami’ar Cambridge.”

“Ina son amfani da wannan dama wajen godewa tsohon shugaba Obasanjo da ya bani shawaran zuwa jami’ar don karatu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here