Wanda Atiku ya Zaba a Matsayin Mataimaki a Zaben 2023
Bayan dogon lokaci ana kace nace, wasu bayanai sun tabbatar da cewa Atiku Abubakar ya zaɓi wanda ya ke so ya zama abokin takararsa.
Jam’iyyar PDP ta tsinci kanta cikin ƙaƙanikayi game da wanda zai zama mataimaki, sai dai Gwamna Wike da Okowa ne a sahun gaba.
Yayin da kwamitin da PDP ta kafa domin lamarin ya zaɓi gwamna Wike, majiya kusa da Atiku tace ɗan takaran ya fi son gwamna Okowa.
Abuja – Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, zai gabatar da ɗan takarar mataimaki da ya zaɓa a tsakar ranar nan, Alhamis 16 ga watan Yuni, 2022.
Makusantan tawagar yaƙin neman zaɓen Atiku sun bayyana cewa za’a sanar da zaɓin da ƙarfe 12:00 na rana kuma bayan haka Kwamitin da aka kafa zai tantance shi.
Read Also:
Hakan ya biyo bayan jerin taruka da ɗan takarar ya gudanar da manyan ƙusoshin jam’iyya jiya Laraba da daddare.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa har zuwa yau Alhamis da safe gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, shi ne zaɓin Atiku Abubakar na ƙarshe.
Wani na kusa da kungiyar Kanfe ɗin Atiku ya ce:
“Indai ba canjin zaɓi aka samu a mintin ƙarshe ba, Gwamna Okowa ne za’a sanar da safiyar nan amma kunsan cewa a siyasa minti ɗaya ma yana da tsayi.”
Kakakin ɗan takarar na PDP, Paul Ibe, ya ƙi tsokaci kan sunan ɗan takarar mataimaki da aka zaɓa, inda ya faɗa wa jaridar cewa su jira a sanar a hukumance.
Ive ya ce:
“Abinda zan iya cewa shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa ya damu ya kammala batun zaɓo abokin takara saboda ya maida hankali kan mataki na gaba na kwace mulki daga hannun APC.”
“Wanda ɗan takarar zai zaɓa ba bu tantama kowane ɗan Najeriya mai ƙishi zai ji daɗinsa a cikin zuciya.”