Attajirai 5 da Suka Fi Tallafawa Masu Karmin Karfi a Najeriya

 

Attajirai da dama suna amfani da dukiyoyinsu domin tallafawa masu karamin karfi ba tare da an roke su ba, mafi yawancinsu suna kafa gidauniya da sunansu ko na kamfanoninsu ko kuma wasu lokutan a boye suke taimakon.

Legit.ng ya haska fitilarsa kan wasu attajiran yan Nigeria da yan kasuwa da ke amfani da dukiyoyinsu domin farantawa jama’a rai ta hanyar basu tallafi.

1. Aliko Dangote

Dan kasuwa Aliko Dangote shine na farko a jerin yan Nigeria da suka fi yin kyauta da dukiyarsu.

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka ya mallaki kimanin Dala biliyan 11.6 a cewar Forbes, yana da hanyoyi daban-daban da ya ke fitar da kudi don tallafawa jama’a.

Dangote, ta hanyar amfani da gidauniyarsa na Aliko Dangote Foundation, ADF, da aka yi wa rajista a 1994 ya kashe fiye da Dallar Amurka miliyan 100 wurin ayyukan taimakawa jama’a a cewar Persecondnews.

A baya bayan nan ADF ta kaddamar wani shirin tallafawa mutane da harin yan bindiga ya shafa a Zamfara inda aka rabar da Naira biliyan 3.924 ga mata da matasa 390492 a jihohin Nigeria a matsayin jari.

2. Tony Elumelu

Shugaban United Bank for Africa, UBA, Tony Elumelu mutum ne da ya yi fice wurin tallafawa jama’a.

Ya taimakawa matasa masu sana’a da yawa ta hanyar amfani da gidauniyarsa na Tony Elemelu Foundation, TEF, da aka kafa a 2010.

A karkashin gidauniyar an ware kimanin Dala miliyan 100 domin binciko da taimakawa matasa 10,000 kawo yanzu. Baya da wannan akwai wasu ayyukan da ya ke yi da dama na taimakon mutane.

3. T.Y. Danjuma

Tsohon Janar na Soja mai murabus, tsohon ministan tsaro kuma shugaban kamfanin South Atlantic, T.Y. Danjuma na daya daga cikin mutanen da ke tallafawa mutane sosai a Nigeria.

Dan kasuwar, ta hanyar amfani da gidauniyarsa na TY Danjuma Foundation yana samar wa yara da matasa ilimi, magunguna da wasu ababen rayuwa kyauta.

Gidauniyarsa kuma tana hadin gwiwa da wasu kungiyoyin masu taimakon mutane wurin tallfawa mutanen karkara.

4. Folorunso Alakija

Folorunso Alakija biloniyar yar kasuwa ce mai zuciyar taimakawa mutane.

Gidauniyarta na Rose of Sharon Foundation wanda ke mayar da hankali wurin taimakawa marayu da matan da mazajensu suka rasu ya samar da gidaje 630 ga matan da mazansu suka rasu sannan ya basu tallafi na lafiya da lauyoyi kyauta.

5. Toyin Saraki

Toyin Saraki, matar tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ta hanyar amfani da gidauniyarta na Wellbeing Foundation Africa (WBFA) ya taimakawa iyalai da dama ta hanyar karfafawa mata gwiwa da basu jari a garuruwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here