Ned Nwoko: Gara in Auri Mai Mata Akan Nayi Mu’amala Mara Kyau – Phyllis Thompson

 

Wata mata ‘yar kasuwa daga kasar Zambia ta wallafa hotunanta tare da biloniya Ned Nwoko.

A wallafar ta ce gara ta shiga a mace ta 7 domin ta san matsayinta kuma ana son ta aka aura.

Ta ce alaka mara kyau wacce babu mutunci a ciki tare da zargi bata dace da mace kamar ta ba.

Wata mata ‘yar kasuwa daga kasar Zambia ta ce a maimakon zaman haka gara ta shiga a matsayin mace ta bakwai tunda ta san matsayinta da kuma soyayyar da ake mata, a kan ta kasance da wanda bai dace ba sannan babu mutunci.

Phyllis Thompson ta sanar da hakan ne a wata wallafa da tayi a shafinta na Facebook tare da wallafa hotunanta tare da mijin Regina Daniels, Ned Nwoko.

Ta kara da cewa hankalinta ya dauku da neman kudi kuma yadda ake mutunta ta tamkar sarauniya yasa bata bukatar komai a rayuwarta.

Kamar yadda ta wallafa, “Gara in kasance da auren mai mata kuma in san matsayina sannan a so ni, mutunta ni tare da bani kariya a maimakon alaka da mutanen da bai dace ba sannan babu mutunci.

“Ina fama da ayyukan kuma ana mutunta ni tamkar sarauniya. Bana bukatar komai a rayuwata. Ina bi ta kan abinda ya dameni. Idan kina yin abubuwan da suka dame ki tare da cigaba a rayuwarki, baki da lokacin duk wani rikici.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here