Rikicin Rasha da Ukraine: Australia ta Haramta Shigar da Duwatsu Masu Daraja Rasha

 

Australia ta haramta fitar da duwatsun alumina da bauxite masu daraja zuwa Rasha saboda mamayar da ta yi wa Ukraine.

Australia ce ƙasar da ke samar wa Rasha kashi 20 cikin 100 na dutsen alumina da take amfani da shi.

Wannan takunkumi kari ne kan wanda kasar ta dauka a karshen watan jiya a kan Rasha.

A ranar Juma’a ma Australia ta sanya takunkumi ga wani dan kasuwar Rasha Oleg Deripaska da ya mallaki wani bangare na masana’antar sarrafa alumina a Queensland.

A bangare guda kuma, Australia za ta bai wa Ukraine karin tallafin dala miliyan 22 na kayan agaji da karin dala miliyan 21 domin tallafa wa sojin ƙasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here