Babu Jami’in da za a Bari ya Shiga Harkar Zabe ko Kuma ya Marawa Wani ‘Dan Takara Baya – Janar Faruk Yahaya
Abubuwa na iya tabarbarewa a Najeriya yayin da ake shirye-shiyen babban zaben 2023 da ke kara gabatowa.
Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Faruk Yahaya ne ya yi wannan gargadi a lokacin da yake jawabi ga Kwamandojin sojoji a jihar Rivers.
Yahaya ya yi hasashen cewa wasu yan siyasa na iya daukar yan baranda don kawai su cimma manufofinsu na son zuciya.
Rivers – Gabannin babban zaben 2023, Shugaban hafsan soji na kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya ya yi hasashen wasu lamura da ka iya tasowa daga bangaren siyasar kasar.
Yahaya ya bayyana cewa abubuwa na iya tabarbarewa a bangaren siyasa a fadin yankunan kasar.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni a Port Harcourt, da yake jawabi a wani taron kwamandojin rundunar, Daily Trust ta rahoto.
Shugaban sojin ya gargadi dakarun rundunar da su guji shiga harkar siyasa yayin da zaben 2023 ke gabatowa.
Read Also:
Ya ce babu jami’in da za a bari ya shiga harkar zaben ko kuma ya marawa wani dan takara baya kamar yadda yake bisa dokar aikin.
Jaridar The Nation ta nakalto Yahaya yana cewa:
“Saboda haka, Ina so na tunatar da dukkanin kwamandoji cewa yayin da lokacin zabe ya gabato akwai yiwuwar bangaren siyasar ya yi tsami a fadin yankunan kasar.
Hada kai da yan dabar siyasa; amfani da kalaman kiyayya da sauran abubuwa marasa amfani daga bangaren yan siyasa masu son zuciya da magoya bayansu zai iya haifar da rashin tsaro a cikin kwanaki masu zuwa.
“Ina umurtan kwamandoji a dukkan matakai da su tabbatar da ganin cewa an wayar da kan dakarun rundunar yadda ya kamata kan kauracewa siyasa da nisantan duk wani rikici na siyasa.
“Da wannan, ya zama dole dukkanin Jami’an soji su yi aiki bisa iyakar doka; su bi tsarin da aka shimfida na aiki da ka’idojin gudanarwa na zabe a 2023.”
Yahaya ya ce rundunar za ta yi amfani da tsarin aiki mai tsauri da amfani da karfin hadin gwiwa na dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a cikin kwanaki da makonni masu zuwa.
Ya ce an shirya taron ne don karawa juna sani da kuma samar da mafita mai dorewa kan kalubalen da ke fuskantar ayyukan da ke gudana a kasar.