Babu Wani Muƙami da a Yanzu Nake Nema a Rayuwata – Bafarawa

 

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Dakta Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce babu wani muƙami da a yanzu yake nema a rayuwara.

A hirarsa da BBC Bafarawa ya ce a yanzu duk wani mai mulki da ai kai wa ziyara, zai je ne tsakaninsa da Allah ba don wani abu da zai samu ba na muƙami.

”Babu abin da na ke so a yanzu, bayan gamawa lafiya”.

Hirar na zuwa ne bayan ziyarar da ƙungiyar tsoffin gwamnonin 1999 wadda Bafarawa ke cikinta, da suka yi zamani da shugaban ƙasar Bola Tinubu, lokacin da yake gwamnan jihar Legas na cikin waɗanda suka ziyarce shi a `yan kwanakin nan.

A filin mu na gane mani hanya wannan makon, Ibrahim Isa ya tattauna da tsohon gwamnan na jihar Sokoto, kan ziyarar tasu da wasu batutuwa da suka shafi siyasar Najeriya da ta jihar Sokoto

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here