Babu Mulkin Karba-Karba a Kundin Tsarin Mulkin APC – Buba Galadima

Ana muhawara a APC game da ko har yanzu akwai batun yarjejeniyar mulkin karba-karba.

Alhaji Buba Galadima ya tabbatar da cewar akwai yarjejeniyar mulkin karba-karba a tsakanin wasu jiga-jigan APC.

Galadima, tsohon na hannun daman Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci shugabannin APC da su riki yarjejeniyar.

Shugaban sabuwar jam’iyyar Reformed All Progressives Congress, R-APC, Alhaji Buba Galadima ya kaddamar da cewar a yayin kafa jam’iyyar, akwai yarjejeniyar mulkin karba-karba da shugabannin jam’iyyar mai mulki suka yarda da shi.

Galadima ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Sun wanda aka wallafa a ranar Asabar, 2 ga watan Janairu.

Sai dai, ya bayyana cewa kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin APC, babu wata kalma na mulkin karba-karba a cikinta.

Kalamansa:

“Na ji daga majiya abun dogaro cewa akwai yarjejeniyar dattak a tsakanin wasu jiga-jigai daga kudu maso yamma da arewa cewa idan kudu maso yamma suka mara masu baya Buhari ya lashe zaben 2015 cewa arewa za ta marawa dan takarar kudu maso yamma baya a 2023.

“Wannan yarjejeniyar dattako ne. Bari na kuma ce alkawari, alkawari ne, kuma idan kayi alkawari ya zama dole ka cika wannan alkawarin.

“Wadanda suka zauna sannan suka amince da wannan yarjejeniyar sune tsoffin gwamnoni biyu daga kudu maso yamma, gwamna mai ci daga arewa, da kuma wani jigon siyasa daga arewa, sune suka sanya hannu a wannan yarjejeniyar. Ya kasance muhimmin yarjejeniya.”

Da aka tambaye shi ko yana cikin yarjejeniyar, ko ya taka wani rawar gani a yarjejeniyar, Galadima ya ce:

“Ba na cikin yarjejeniyar amma wadanda ke cikin yarjejeniyar da suka kulla sun fada mun. Idan mutanen APC na da mutunci, dole ne su cika alkawarinsu. Idan shugabannin jam’iyyar na da gaskiya, dole ne su aiwatar da wannan yarjejeniyar.”

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here