Bada Kwangila: Tsohuwar Shugabar Hukumar NPA, Hadiza Bala Usman ta Mai da Martani
Dakatacciyar shugaban hukumar NPA, Hadiza Bala Usman, ta musanta rahotanni da ke yawo na cewa ita kadai ke iya bada kwangila a NPA.
Kamar yadda ta bayyana a wata takarda, ta ce wannan rahoton na nuna tsabar rashin fahimta, rashin tunani da son bata mata suna.
A cewar tsohuwar shugaban NPA, hukumar ta mallaki kungiya dake duba duk wani bangaren kasuwanci da kadarorinta.
Hadiza Bala Usman, dakatacciyar manajan daraktan NPA ta musanta rahoton kafafen yada labarai na cewa ita kadai ke iya bada kwangila a hukumar yayin da take shugabanci.
Read Also:
A wata takarda da ta saka hannu a ranar Lahadi, 9 ga watan Mayun 2021, Usman ta kwatanta rahotannin da rashin fahimta tare da bacin suna, The Cable ta ruwaito.
A makon da ya gaba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da bala Usman a matsayin manajan daraktan NPA kuma ya amince da nada Mohammed Koko domin ya jagoranci hukumar har sai an kammala bincikenta.
The Cable ta ruwaito dalla-dalla yadda Rotimi Amaechi, ministan sufuri ya shiga ya fita har ya tabbatar da amincewar Buhari wurin dakatar da Bala Usman.
Bala Usman ta ce NPA tana da kungiya wacce koyaushe take yanke hukunci kan dukkan kadarorin da kasuwancin NPA kuma mai dogaro da ra’ayin ‘yan Najeriya.
“Cewa ni kadai nake bada kwangila a matsayin manajan daraktan NPA, akwai son zuciya, rashin fahimta da kuma son bata suna,” takardar tace.