Matsalar Tsaro: Tsohon Gwamnan Sokoto, Bafarawa ya Nuna Damuwarsa Kan Halin da Yankin Yake Ciki
Tsohon gwamnan jahar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya nuna damuwarsa kan halin da al’ummar yankin arewa maso yamma suke ciki.
Bafarawa yace matsalar tsaro ta kai yadda manoma sun kasa zuwa gonakinsu girbin abinda suka noma saboda tsoron yan bindiga.
Ya yi kira ga gwamnan Zamfara da kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, su rinka ziyara zuwa jahohin wannan yanki don ganewa idonsu.
Zamfara – Tsohon gwamnan Sokoto, kuma sanannen ɗan siyasa, Attahiru Bafarawa, yace mutane sun shiga cikin matsin rayuwa a yankin arewa maso yamma.
Bafarawa ya koka kan yanda mutane suka sha wahalar noma amfanin gona amma matsalar tsaro ta hana su zuwa ɗebo abinda suka noma.
Ya kuma ƙara da cewa halin da mutane suka tsinci kansu a yankin Arewa maso yamma musamman Sokoto da Zamfara, ba ya misaltuwa domin ya wuce tunani.
BBC Hausa ta rawaito tsohon gwamnan ya bukaci gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya kai ziyara zuwa wasu sassan jaharsa domin ganin halin da mutane ke ciki.
Read Also:
Hakazalika ya gane wa idonsa irin tasiri ko akasin haka na matakan da ya ɗauka don magance ayyukan tsagerun yan bindiga.
Ko ana faɗa wa shugaban ƙasa halin da mutane ke ciki?
Bafarawa ya bukaci shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kai ziyara waɗannan jahohi ko kuma ya tura amintattunsa domin su gano ainihin abinda ke faruwa.
Tsohon gwamnan yace:
“Ban sani ba makusantan shugaba Buhari suna faɗa masa gaskiyar abinda ke faruwa a jahohin arewa, idan basu faɗar gaskiya to sun cuce mu.”
“Ni ganau ne, manoma na cikin bala’i, domin a halin da ake ciki yanzun suna tsoron zuwa girbin abinda suka noma saboda matsalar tsaro.”
Shin dagaske gwamnati na tallafawa mutane da Abinci?
A cewar tsohon gwamnan, shi dai bai taɓa ganin hakan ba, kuma yana zuwa Bafarawa lokaci bayan lokaci amma ko labarin tallafin bai taɓa ji ba.
“Ya kamata idan shugaba ya kafa doka, to ya sanya kwamiti da zai rinka sa ido wajen tabbatar da dokar na aiki, ko kuma shi dakansa ya rinka bibiyar lamarin.”
“Idan ka bada umarnin a tallafawa mutane da abinci, a matsayinka na shugaba kamata ya yi ka sa a rinka duba ko tallafin na kaiwa ga al’umma ko baya zuwa.”