Bahrain ta Fuskanci Mafi Munin Hare-Hare

Ƙasar Bahrain ta fuskanci mafi munin hare-haren Iran a yau Talata.

Rahotonnin farko sun nuna cewa makami mai linzamin Iran ya faɗa kan wani sansanin soji a yammacin ƙasar.

Bahrain ta ce harin da aka kai sansanin soji na Hamala ya kashe wani mai kwantiragin soji ɗan asalin Moroko, tare da raunata gomman mutane, ciki har da huɗu da ke cikin mawuyacin hali.

Bayanai sun ce duka waɗanda suka jikkata ƴan ƙasar ne ciki har da sojoji.

A ƙasar Bahrain ne Amurka ke da sansanonin sojin ruwa na Fifth Fleet, kodayake an janye duka dakarun ƴan kwanaki kafin fara yaƙin, jiragen ruwansu suka bar wurin.

Bahrain – wadda a wasu lokuta Iran ke kallon ta a matsayin wani yanki nata da ta rasa – ta kasance mafi munin alaƙa da Iran daga cikin ƙasashen yankin Gulf shida.

Sauran hare-haren sun faɗa kan tankunan mai da filin jirgin sama da gidaje.

Mafi yawan al’ummar Bahrain ƴan shi’a ne kuma wasu daga cikinsu na goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kuma ƙasar ta hana ƴan jaridar waje shiga cikinta domin bayar da rahotonnin abubuwan da ke faruwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here