Yadda Sojojin Najeriya Suka Baiwa Tubabbun Boko Haram Abinci ya Kawo Cece-kuce a Kafar Sada Zumunta

 

Kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ta cika da cece-kuce bayan bayyanar wasu hotunan tubabbun.

Boko Haram A cikin hotuna an ga yadda sojojin Najeriya suke baiwa tubabbun kwamandojin Boko Haram abinci.

An samu labarin yadda kwamandojin ‘yan Boko Haram suka yi mubaya’a ga sojojin Operation Hadin Kai.

Cece-kuce sun yawaita a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter bayan bayyanar hotunan sojoji suna baiwa tubabbun kwamandojin mayakan Boko Haram kayan abinci.

Kwamandojin Boko Haram sun zubar da makamansu sannan sun yi mubaya’a ga sojojin Operation Hadin Kai, The Cable ta wallafa.

A wata takarda ta ranar Litinin, Kakakin sojin, Onyema Nwachukwu, ya wallafa hotunan kwamandojin Boko Haram inda yace Musa Adamu, kwararre akan hada bama-bamai cikin ‘yan Boko Haram yana daya daga cikin wadanda suka tuba.

Jawabin rundunar sojoji

Bayan harin kwanannan da rundunar Operation Hadin Kai suka fara bude wa ‘yan Boko Haram na arewa maso gabas wuta babu kakkautawa ya janyo shugaban kwararru a harkar hada bama-bamai, Musa Adamu, wanda aka fi sani da Maka Musa Abuja, da mai binsa a iko, Usman Adamu wato Abu Darda, tare da iyalansa sun mika wuya ga OPHK dake karamar hukumar Bama dake jahar Borno, kamar yadda takardar ta shaida.

Sojojin sun baiwa tubabbun ‘yan ta’addan sababbin kayan sawa, kayan abinci da sauran kayan masarufi cikinsu akwai mayaka 335, mata da yara 746 ciki har da matan Chibok.

Tubabbun ‘yan Boko Haram sun nemi yafiyar ‘yan Najeriya

Tubabbun ‘yan ta’addan sun rike wata takarda wacce a jikinta aka rubuta, “Yan Najeriya ku taimaka kunyafe mana”.

‘Yan Najeriya sun yi martani

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, tuni ‘yan Najeriya suka dinga cece-kuce tare da caccakar gwamnati kan karamcin da take yi wa tubabbun ‘yan Boko Haram.

A cewar wani Samuel wanda yayi tsokaci a Twitter:

Za a tankwasa doka ta yafe musu, gwamnati kuma zata girmama su ta hanyar basu kudin jama’a suyi wadaka dasu.Amma matasan Najeriya da suka yi zanga-zanga an mayar dasu tamkar beraye wadanda za a kama a sakaya a gidan yari wasu kuma a kashe. Haka salon mulkin kasar nan yak.

Wani Easy kuwa cewa yayi:

Wannan ai abin takaici ne

Adedayo Adesuyi yace:

Tubabbun ‘yan Boko Haram dauke da rubutun neman gafara. Ya aka yi suka rubuta?

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here