Shugaban Kasar Nijar ya Bai wa Gwamna Zulum Lambar Yabo
Gwamnan jahar Borno ya karbi lambar yabo mai girma a kasar Nijar saboda jajircewarsa.
Gwamnan ya je kasar ne domin karbar lambar girmamawa, wanda shine na farko da ya fara karba.
Ya samu rakiyar wasu jiga-jigan siyasar jahar ta Borno a yayin karbar wannan babbar girmamawa.
Shugaban kasar Nijar, Mohammed Bazoum ya bai wa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, lambar girmamawa ta kasa mai suna “de Grand Officer dans I`Ordre” sakamakon irin rawar da ya ke takawa a yaki da matsalolin rashin tsaro.
Read Also:
Shugaba Bazoum ya ce girmama Zulum ya zama masa wajibi lidan aka yi a’akari da namijin kokarin da Zulum ke nunawa a yakar Boko Haram, damuwar da yake nunawa kan ‘yan gudun hijira da kokarin sake tsugunar da su a yankunansu da yaki ya lalata.
An gudanar da bikin karrama Zulum ne a birnin Zinder, a wani bangare na bikin ranar yanci da Nijar ke gudanawar a ranar Talata 3 ga watan Agustan 2021, BBC ta ruwaito.
Wannan shi ne karo na farko da wani shugaba a Nijar ke bai wa gwamna a Najeriya irin wannan lambar girmamawa.
Zulum ya je Nijar din ne da rakiyar Sanata kashim Shettima da dan majalisa Mohammed Ali Ndume da kakakin majalisar jihar Borno Mohammed Tahir Monguno da wasu kwamishinoninsa.