Bam ya Tashi da Mambobin IPOB Biyu da Suka Binne
Wasu mutane biyu da ake zargin mambobin haramtaciyar kungiyar IPOB/ESN ne sun yi munanan rauni yayin da wani bam ya tashi a ranar Laraba 1 ga watan Yuni.
Mutanen biyu, a cewar Rundunar Sojojin Najeriya, sun taka bam din da suka birne ne bisa kuskure a hanyoyi a garin Orlu.
Rundunar sojojin ta Najeriya ta bukaci mutanen yankin na kudu maso gabas masu son zaman lafiya su rika sanar da sojojin wuraren da suke zargin an binne bama-bamai.
Jihar Imo – Wani abin fashewa/bam da aka rahoto cewa mambobin kungiyar IPOB/ESN ne suka birne ya fashe, ya kuma yi wa mambobin kungiyar biyu mummunan rauni, rahoton NAN.
Read Also:
A cewar Vanguard, lamarin ya faru ne a kan hanyar Eke Ututu – Orsu a karamar hukumar Orsu a Jihar Imo a ranar Laraba 1 ga watan Yuni.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojoji, Brig Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce:
“Bata garin, sun taka wani abin fashewa da suka birne a baya a kan hanyar karamar hukumar Orlu, yayin da suke kokarin tserewa daga dakarun sojoji da ke farautarsu a yankin.
“Haramtaciyyar kungiyar ta birne bama-bamai da dama a hanyoyin da sojoji ke sintiri amma ba su yi nasarar raunata sojojin ba.
“Muna kira ga mutanen Kudu maso Gabas masu son zaman lafiya su rika sanar da sojoji wuraren da suke zargin an birne bama-baman domin a cire su tare da zubarwa.”