Dalilin da Yasa Ban je Gaban Kotu ba – Abdulrasheed Maina
Abdulrasheed Maina yayi magana da wani gidan rediyo daga inda ya ke kwance.
Tsohon jami’in gwamnatin yace jinya ta hana shi fitowa yayin da ake ta nemansa.
Ya zargi EFCC da rashin gaskiya, sannan yace an hana shi ganin shugaban kasa.
Abdulrasheed Maina wanda ake nema a kotu ya fito ya bayyana cewa bai tsere ba, ya na nan ya na jinya asibiti, sannan ya fadi wasu abubuwa da ba a sani ba.
Maina ya ce: “Likita ya rubuta takarda cewa bani da lafiya, kafa ta ba lafiya, za ayi mani aiki, aka yi mani aiki, sai kawai ina zaune a asibiti na ji ana nema na.”
“Ana ta cigiya ta kamar ya?”
Read Also:
“Shi Sanatan da ya sa mani hannu, ‘dana ya fada masa ‘Ka zo muje ka ga mahaifina a asibitin da yake’, ya ki zuwa, kuma ya zai fada wa kotu bai san inda na ke ba?”
Maina ya ce maganar Ali Ndme ba daidai ba ce, ko kuma wadanda suka fada masa sun yi masa karya.
Tsohon jami’in gwamnatin ya ke cewa: “Mu da muke gyara, zamu kawo gyara, muna taimakon kasa, an yi mana katanga da shugaban kasa, an bata mu.”
“An je ana amfani da EFCC a kanmu, wasu ma’aikatan EFCC da suka karbi kudin na sansu, idan lokaci ya yi zan fadi sunayensu, al’umma su sansu.” Inji Maina.
Abdulrasheed Maina ya tambayi ina N1.6tr da kuma N1.3tr da daruruwan gidaje da ya karbe daga hannun barayin gwamnati a lokacin Jonathan da shugaba Buhari.
Maina ya ce yana so ya so shugaban kasa ya san halin da ake ciki domin an yi masa shamaki da shi.
A karshe a hirar da aka yi da shi a gidan rediyo, tsohon shugaban kwamitin binciken kudin fansho na kasar, ba zai tsere ba, ya na nan a Najeriya yana jinya.