Bani da Hurumin Raba Kujerun Siyasa Irin na Shugaban kasa ko Mataimakin Shugaban Najeriya – Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi

 

Kwamitin fito da yadda za ayi rabon kujeru na jam’iyyar PDP a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba, ya gana a Enugu, babban birnin jahar Enugu.

Ifeanyi Ugwuanyi, gwamnan jahar Enugu, wanda kuma shine shugaban kwamitin, ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai jawabi.

A cewarsa, PDP ita ce jam’iyya guda da za ta iya isar da kyakkyawan shugabanci ga Najeriya.

Enugu, Enugu – Kwamitin fito da yadda za ayi rabon kujeru na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 23 ga Satumba, ya ce ba shi da hurumin raba kujerun siyasa irin na shugaban kasa ko mataimakin shugaban Najeriya.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa gwamnan jahar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, wanda kuma shine shugaban kwamitin, ya fadi hakan ne a cikin jawabinsa a yayin taron su na farko a gidan gwamnati, Enugu.

Legit.ng ta tattaro cewa shugabancin jam’iyyar ne ya kafa kwamitin domin rabawa shiyoyi kujerun PDP na kasa gabanin babban taronta da ake shirin gudanarwa a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoba.

Ya ce:

“Kwamitinmu ya tsaya ne kawai ga ofisoshin zartarwa na PDP na kasa wanda za a fafata da su a babban taron PDP na 2021 da aka shirya yi a karshen Oktoba 2021. Ba za mu raba kujerun siyasa irin na shugaban kasa ko mataimakin shugaban Najeriya ba.”

Ya kara da cewa aikin kwamitin zai ba da gudummawa mai yawa “da za su taimaka wa PDP wajen cimma kyawawan manufofin magabatan mu.”

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnan ya ƙarfafawa membobin kwamitin gwiwa da su kasance masu faɗin gaskiya da buɗe ido a cikin shawarwari da muhawararsu, da nuna daidaito tare da girman aikinsu.

Ugwuanyi ya ci gaba da cewa:

“An zabi membobi da shugabancin wannan kwamitin a hankali saboda ya kunshi gogaggu, kwararru da fitattun ‘yan Najeriya wadanda ke da burin sake canza PDP don taka rawar ganinta ba wai a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ba amma don gina jam’iyyar da za ta tabbatar da muradin ‘yan Najeriya cewa bayan wuya sai dadi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here