Mutumin da Banki ya yi Kuskuran Tura wa N24bn ya Shiga Hannu

 

Ana tuhumar wani mutumi bisa zargin satar zaune bayan kashe miliyan N750m da banki ya tura asusunsa bisa kuskure.

Bankin ya yi kuskuren sanya kuɗi biliyan N24bn a asusun mutumin bisa kuskure sakamakon wata ‘yar tangarɗa.

Jami’an yaƙi da masu zamba ne suka damƙe mutumin kuma sun samu nasarar kwato tsabar kuɗi naira miliyan N450m a cikin gidansa.

Wani mutumi mai suna Joel Julien daga Trinidad ya shiga hannun jami’ai bisa zargin sace makudan kuɗi daga bankinsa bayan tafka babban kuskure.

Bisa tsautsayi, bankin ya antaya kudi sama da biliyan N24bn a asusun mutumin amma ganin tamkar ya tsinci dami a kala, mutumin ya ci gaba da sha’aninsa da kuɗin.

A rahoton da Jamian Observer ta tattara, kafin Mista Julien ya shiga hannu, har ya yi shagalinsa da miliyan N750m daga cikin zunzurutun kuɗin da aka tura masa bisa kuskure.

Za’a gurfanar da mutumin gaban Kotu ya yi bayani

A halin yanzu jami’an ‘yan sanda na tuhumar Julien da satar zaune kuma zai gurfana gaban Kotu domin ya yi bayanin dalilin da ya sa ya taɓa kuɗin da ba na shi ba.

A rahoton Guardian, yan sanda sun gano cewa bankin ya fahimci kuskuren da ya tafka ne bayan nazari kan bayanan ayyukan da suka gudana.

Sun gano cewa tangarɗar da na’urarsu ta samu ya yi sanadin tura kuɗi dala 32,347,308.55 zuwa asusun Julien.

A rahoton Guardian, yan sanda sun gano cewa bankin ya fahimci kuskuren da ya tafka ne bayan nazari kan bayanan ayyukan da suka gudana.

Sun gano cewa tangarɗar da na’urarsu ta samu ya yi sanadin tura kuɗi dala 32,347,308.55 zuwa asusun Julien.

Yan sanda sun ce Julien ya yi amfani da kuɗin ta hanyar zuwa na’urar ATM ya zare tsabar kuɗi da kuma amfani da katinsa wajen sayayya a shaguna.

Mutumin ya kashe miliyan N750m daga cikin kuɗin a tsakanin 18 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamban shekarar da ta gabata, inji yan sanda.

Meyasa ya ƙi maida kuɗin?

Bankin ya yi ƙoƙarin dawo da kuɗin daga hannun Julien ta hanyar maslaha amma ya ƙi ba da haɗin kai, bisa haka ya kai ƙararsa ga jami’an yaƙi da zamba.

Yayin bincike jami’an suka yi ram da Julien kuma suka kwato tsabar kuɗi dala 600,501 a cikin gidansa.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here