Dantata ya Kirkiri Sabon Bankin Zamani na Yanar Gizo Mai Suna Kayi
Najeriya ta sake samun sabon bankin zamani na yanar gizo wanda zai taimaka wurin kawo sauki a harkar cinikayya na kudade.
Sabon bankin mai suna Kayi wanda Alhaji Saadina Dantata ya kirkira ya samu sahalewar wasu kasashe na hannun jari kamar Saudiyya.
Sabon bankin na dan kasuwar da ke Kano zai fafata da sauran bankunan yanar gizo kamar su Kuda da Opay da Moniepoint da sauransu.
FCT, Abuja – Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Bosun Tijjani ya kaddamar da wani bankin zamani na yanar gizo mai suna ‘Kayi Bank’.
Bankin wanda attajirin dan kasuwa, Alhaji Saadina Dantata ya dauki nauyi an kaddamar da shi a Abuja a makon da ya gabata.
Meye kudirin bankin Kayi na Dantata?
Read Also:
Legit ta tattaro cewa bankin Kayi kasashe da dama kamar su Daular Larabawa da Turkiyya da Saudiyya sun zuba hannun jarinsu a ciki.
Da ya ke magana, Dantata ya ce an samar da kamfanin ne don shawo kan matsalar fasaha da tsaro da kuma inganta jin dadin kwastomomi.
Ya ce:
“Mu na inganta rayuwar murane a fadin Nahiyar Afirka wurin samar da cinikayya ta kudade cikin sauki.
“Burinmu shi ne samar da asusun bankuna ga wadanda ba su da shi da wadanda ke kasashen ketare.”
Wane amfani bankin Kayi zai yi ga al’umma?
Minista sadarwa ya yabawa mamallakin bankin Kayi inda ya ce hakan zai karawa gwamnatin Bola Tinubu karfi wurin tabbatar da samar da ayyukan yi.
The Nation ta tattaro cewa ministan ya godewa kamfanin wurin samar da sauki ga masu tasi da adaidaita sahu.
A tsarin kamfanin, zai samarwa masu tasi din saukin yadda za su sayi mai a wasu gidaje tare da biyan kudin bayan kwana daya don rage radadin cire tallafi.