Barayi Sun Shiga Gidan Shugaban Ma’aikatar Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari Dake Aso Rock

 

Labari da duminsa na nuna cewa wasu barayi sun yi yunkurin fasawa cikin gidan shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, dake Aso Rock, birnin tarayya Abuja.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Litinin.

Garba ya bayyana cewa barayin basu samu nasarar satan komai ba.

“Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya tabbatar da cewa an yi “wawan yunkurin” yi masa fashi a gidansa misalin karfe 3 na daren nan amma basu samu nasara ba,” Garba Shehu yace. “Farfesa Gambari…ya ce babu wani abin damuwa.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here