Kungiyar Barcelona za ta Rage Yawan Kashe Kudade ga ‘Yan Wasan
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta za ta kafa dokar hana ‘yan wasa karin kumallo don rage kashe kudade.
A bayyane ya ke Barcelona na shan daka tare da kame-kame wurin cinikin ‘yan wasa cikin shekarun nan.
Legit.ng Hausa ta ji ta bakin wasu masoya kwallon kafa da ke goyon bayan kungiyoyin kwallon kafa daban-daban.
Barcelona, Sifaniya – Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona za ta cire tsarin karin kumallo ga ‘yan wasa don rage yawan kashe kudade.
Wani rahoto da Relevo ta fitar, ya tabbatar cewa kungiyar ta yanke shawarar cire karin kumallo ga matasan ‘yan wasa.
Me Barcelona ta ce?
Rahoton ya kuma ce mafi yawan ‘yan wasa ba sa samun karin kumallon, hakan ya ba wa shugaban kungiyar, Joan Laporta yanke shawarar cire tsarin karin kumallon da cewa ana kashe kudade babu adalci.
Transfer News Live ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, Barca a kullum kokarin rage yawan kashe kudade ta ke, hakan ne ma ya sa ta daukar wannan mataki.
Ta ce ba ko wane dan wasa ba ne ke samun karin kumallon inda kungiyar ta ga hakan kawai kashe kudade ne ba tare da adalci ba.
Wane hali Barcelona ke ciki?
Ba a boye ya ke ba, Barcelona na shan daka idan aka kwatanta da sauran kungiyoyin kwallon kafa.
Read Also:
Wannan yanayi na matsin tattalin arziki da su ke ciki ya saka kungiyar daukar wasu matakai da ba a saba gani ba don rage kashe kudade a kungiyar.
A kakar wasa ta 2021, dole su ka bar shahararren dan wasansu, Lionel Messi barin kungiyar saboda sun gagara sabunta kwantiraginsa.
Kungiyar ta yi kokarin dawo da Messi don ci gaba buga tambola amma hakan ya ci tura saboda gagara samun kudin da za su biya.
Martanin mutane kan tsarin na Barcelona
Legit.ng Hausa ta ji ta bakin wasu magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa daban-daban.
Aminu Garba Umar ya ce shi ya na goyon bayan wannan mataki dari bisa dari inda ya ce wannan ba wata matsala ba ce.
Ya ce duk lokacin aka samu abin da ake so za a iya dawo da tsarin.
Ya ce:
“An yi haka ne don kungiyar ta tsaya da kafafunta, a baya da ba sa cikin matsala ai ba a yi haka ba.
“Duk lokacin da komai ya dawo dai-dai kungiyar ta farfado za ta iya mayar da wannan tsari.”
A martanin Ibrahim Yahaya ya ce wannan tsari bai yi ba, idan za su nemi bashi kawai su nemo.
A cewarsa:
“Wannan wane irin tsari ne?, Idan za su nemi bashi kawai su ci, ai hakan ya na kashe kwarin gwiwar ‘yan wasa.
“Babu wani dan kwallon gaske da zai je kungiyar saboda abun kullum baya ya ke kara yi.”
Shamsuddeen Madrid ya ce wannan ai abin kunya ne, wane tasiri kudin karin kumallo zai yi wa kungiyar.
Ya ce:
“Gaskiya wannan abin kunya ne, babu abin da wannan zai kara musu, watakila a baya ma sun cire wasu abubuwa da ban sani ba.”