Sheikh Dahiru Bauchi ya Bayyana Goyan Bayansa ga Atiku Abubakar

 

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, shugaban darikar Tijjaniya ya ce, dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar zai zaba a zaben ranar Asabar.

Fitaccen malamin ya bayyana goyon bayan Atiku ne a sakon da ya ba mabiyansa, Daily Trust ta ruwaito.

“Ba a saran mumini a sau biyu a wuri guda, wasu mutane suna cewa wai a zabi wanda zai ci gaba daga inda suka tsaya, bamu ji dadin inda suka tsaya ba.

“Da yawan mutane na sun ce za su zabi Atiku, nima ba zan bar mutane na ba, zan kasance tare da mutane na don ganin abin da Allah zai yi. “Muna rokon Allah ya ba Najeriya shugaba na gari wanda zai saukake dukkan kuncin Najeriya da kuma kawo ci gaba.”

Shugaban gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Ibrahim Dahiru Bauchi ya tabbatar da wannan matsaya ta Shehi ga jaridar Daily Trust.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here