Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa ya Yanki  Jiki ya Zube a Banquet Hall Villa

 

Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa ya yanki jiki ya fadi a bikin ranar kasa ta uku a Banquet Hall Villa, Tribune Nigeria ta rawaito.

Bawa wanda ke isar da sakon fatan alheri ba zato ba tsammani ya carke, ya koma kan kujerarsa, ya yanki jiki ya zube.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Pantami, da wasu manyan mutane sun rike shi, bayan wani lokaci, aka yi masa jagora ya fita daga zauren taron.

Karin bayani na nan tafe..

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here