Dirakta Janar na Ofishin Manajin Basussukan Najeriya ta Bayyana Bashin da Ake Bin Najeriya
Biyo bayan maganar buga N60bn don rabawa gwamnoni, DMO ta bayyana bashin da ake bin Najeriya.
Gwamnan CBN ya ce an buga kudin ne don baiwa gwamnoni rance Dirakta Janar na Ofishin manajin basussukan Najeriya DMO, Patience Oniha, ta ce basussukan da ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jahohin yanzu ya kai N33.63 trillion.
A jawaban da ta saki a shafin sadarwanta na Tuwita, Oniha ta ce jita-jitan da ake yadawa kan adadin bashin da ake bin Najeriya yasa ta wallafa jerin basussuka.
Read Also:
A cewarta, “yana da muhimmanci in fayyace cewa wannan bashin na gwamnatin tarayya ne, birnin tarayya, da jahohin Najeriya 36,” “Bashin ba na gwamnatin tarayya bane kadai, gwamnonin jahohi da birnin tarayya na karban bashi.”
“A bangaren gwamnatin tarayya, adadin bashin da aka karba ya karu ne saboda fadin farashin danyen mai a 2015.”
“Amma a kasafin kudin 2018 zuwa 2020, adadin basussukan sun ragu.” “Abin takaici, illar annobar COVID-19 kan kudin shiga ya sabbaba tashin basussukan.”
Za ku tuna cewa a karshen shekarar 2020, DMO ta ce bashin da ake bin Najeriya ya kai N32.9tr.