Bincikar Abba Kyari: Kwamitin Bincike ta Mika Rahoton ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda
Kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar Abba Kyari ya gama bincike, ya kuma mika rahoto ga IG.
Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan da aka dakatar da Abba Kyari bisa zargin rashawa.
A halin yanzu, ba tabbatar da menene ke cikin rahoton ba, amma dai an mika shi Sufeto janar na ‘yan sanda.
Kwamitin Bincike na Musamman ya mika rahotonsa ga Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, makonni biyu bayan da aka umarce shi da ya binciki tsohon Shugaban rundunar IRT kuma Mataimakin Kwamishinan’ Yan sanda, Abba Kyari.
Kwamitin na mutum hudu karkashin jagorancin Mataimakin Sufeto -Janar na ‘yan sanda mai kula da sashin binciken manyan laifuka na rundunar, Joseph Egbunike, ya mika sakamakon binciken ga IG ranar Litinin 16 ga watan Agusta.
A baya mun rahoto cewa, hukumar FBI ta kasar Amurka ta zargi Abba Kyari da hannu cikin wata damfara da Abbas Ramon (Hushpuppi) ya yi kan wani dan kasuwar Qatar, Punch ta ruwaito.
Read Also:
Domin bincika lamarin, IG a ranar 1 ga Agusta ya ba da shawarar dakatar da Abba Kyari ga Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan sanda, daga ranar 31 ga Yuli, sannan ya kafa kwamiti don bincika zargin da ake yi masa.
Yaya zaman ya kasance?
A yayin zaman ta, Kyari ya bayyana sau da dama a gaban kwamitin inda ya yi watsi da zargin hada baki da Hushpuppi don damfarar dan kasuwar na Qatar.
An tattaro cewa zaman kwamitin tare da Kyari ya kasance cikin annashuwa, lamarin da ya baiwa Kyari kwarin gwiwar cewa za a wanke shi daga zargin, in ji rahoton Reuben Abati.
Majiyoyi sun ce Egbunike da Kyari suna da dangantaka ta dogon lokaci tunda tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne a sashen asusun ‘yan sanda inda ya yi aiki sama da shekaru 15.
An gano cewa kwamitin ya gabatar da rahoton a makon da ya gabata amma IG ya ki amincewa da shi saboda ya yi wa Kyari sassauci.
Wata majiya ta ce:
“Kwamitin ya kammala bincikensa sannan ya mika rahotonsa ga IG a ranar Alhamis ko Juma’a da ta gabata amma IG ya ki amincewa. Bai gamsu da sakamakon kwamitin da shawarwarinsa ba.”