Mun Biya Dukkan Ma’aikatan N-Power Haƙƙinsu –  Sadiya Umar Farouq

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu mai binta bashi daga cikin ma’aikatan Npower da suka gama aiki.

Ministar ma’aikatar jin kai da walwala, Sadiya Farouq, itace ta bayyana haka, tace an biya ko wane ma’aikaci haƙƙinsa.

Ta kuma ƙara da cewa yanzun haka ana cigaba da tantance ma’aikatan da za’a ɗauka a runkunin C.

Gwamnatin tarayya tace ta biya dukkan ma’aikatan N-Power haƙƙinsu da aka riƙe a cewar ministan jin kai, Sadiya Farouq, kamar yadda The nation ta ruwaito.

Kusan ma’aikatan npower 14,000 daga rukunin A da B, waɗanda suka gama aikin su a shekarar data gabata ne suke bin gwamnati albashin su na watanni 4.

Ministar ma’aikatar jin ƙai da walwala, Sadiya Farouq, ta bada umarnin duk wanda abun ya shafa ya kai rahoto ga shugaban npower na jaharsa domin tantancewa.

Ministan ta bada wannan umarnin ne a wani ɓangare na ƙoƙarinta wajen ganin an biya waɗanda aka riƙewa albashinsu.

Yayin da take jawabi a wurin wani taron ƙara wa juna sani da ma’aikatarta ta shirya kan ‘rahotannin kafafen sada zumunta’ Minista tace:

“Bana tunanin muna da wata matsala da ma’aikatan npower, mun riga mun warware komai tsakanin mu da Akanta janar na ƙasa (AGF).”

“Ya ɗauke mu dogon lokaci amma daga ƙarshe mun cinma manufa, Mun biya dukkan ma’aikatan npower bayan dogon bincike.”

“Yanzun ma’aikatar mu zata cigaba da aikin ɗaukar ma’aikata a shirin npower na rukunin C, Mun kasa shi zuwa gida biyu, zamu ɗauki mutum 500,000 da farko Sannan daga baya mu ƙara kamar haka.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here