‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kai Wa ‘Yan Sandan Najeriya Hari a Jahar Borno

Yan ta’addan Boko Haram sun kai wa yan sandan Nigeria hari a Borno.

Sun kwace motoci biyu na yan sanda a yayin harin.

Hakan ya faru ne yayinda suka kai hari chek point din yan sandan.

Kungiyar ta’addan Boko Haram ISWAP, masu lakani da Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, sun ragargaza motoci biyu da kungiyar ta kwato daga yan sandan Nigeria.

A wani jawabi da kungiyar ta saki wanda SaharaReporters ta gani ranar laraba, sun kwaci motocin ne yayinda kungiyar ta kai hari wani chek point din yan sanda a hanyar Maiduguri-Chabal-Magumeri a jahar Borno.

Kauyen Chabal a karamar hukumar Magumeri yana da kilo mita 22 daga tashar Maimalari, 7 na marabar sojojin Nigeria a Maiduguri.

A jawabin da yan ta’addan suka saki sun bayyana cewa sunyi garkuwa da yan sanda da mutane da yawa a yayin harin.

A baya mun samu labari daga SaharaReporters yadda yan ta’addan suka kashe yan sanda biyu da wani mutum a kauyen Chabal.

“Yanzu muka samu labari cewa yan ta’addan Boko Haram sun kai wa wasu yan sanda hari a kauyen Chabal. An kuma harbi wani dan sa kai.

An tura Sojoji daga Maimalari zuwa wajen,” wata majiya daga sojoji ta fadawa SaharaReporters ranar Lahadi.

A watannin baya, yan ta’addan sun sha san farmakar jami’an tsaro.

Mutane sama da 30,000 sun mutu a sanadiyyar Yan ta’addan Boko Haram sannan sun raba miliyoyin mutane da gidajensu a jahohin Adamawa, Borrno da Yobe.

Bukatar su, suna san kalifa na musulunci a arewacin Nigeria.

Yan ta’addan sun kuma lalata wani sabon makamin yaki da suka kwato daga sojojin Nigeria wancan watan.

Sun kuma lalata wani FV103 Spartan APC duk da suka kwato a wajen sojoji.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here