‘Yan Boko Haram Sunyi Garkuwa da Ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya
Boko Haram sun sace wani Ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya a hanyar Maiduguri a safiyar Asabar.
An kama ma’aikacin ne tare da wasu mutum da aka sake su daga baya.
Majiya ta ruwaito cewa maharan sun kai hari ne kan matafiyan
‘Yan ta’addar Boko Haram sun sace wani babban mataimaki na kariya a Hukumar Kula da’ Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Alooma, a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, Jihar Borno.
Read Also:
PRNigeria ta tattaro cewa maharan sun kaiwa wasu ayarin matafiya hari a kusa da kauyen Matari tsakanin Minok zuwa hanyar Jakana inda aka yi garkuwa da Alooma da misalin karfe 8.30 na safiyar Asabar.
Wata majiya ta bayyana cewa maharan wadanda suka fito sanye da kayan sojoji sun sanya shingen kan hanya a kan babbar hanyar da motocin Hilux guda uku da babura.
Majiyoyin sun ce: “Yayin da ake binciken fasinjojin, Idris ya yi kokarin jefa katin shaidarsa amma ana kan haka, sai daya daga cikin maharan ya ganshi. Daga nan aka nemi ya sauka daga motar tare da wasu fasinjoji biyu, yayin da aka nemi sauran fasinjojin da su ci gaba da tafiya.
“Daga baya an saki fasinjojin biyu a kan cewa su talakawa ne sosai kuma ba su da wani amfani da za a sace su.”