Hare-Haren Boko Haram: Gwamnan Jahar Borno da Sanatocin Jahar Sun Ziyarci Shugaban Hafsun Sojoji a Abuja

 

Gwamnan jahar Borno ya ziyarci shugaban hafsun sojojin a babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnan ya kai ziyar ne ga shugaban a wata tawaga da ya hada ciki har da sanatocin jahar.

Ya kuma ziyarci shugaban sojin kasa na Najeriya kan batun hare-haren Boko Haram a Borno.

Gwamnan jahar Borno, Zulum, a ranar Litinin, ya jagoranci sanatocin da ke wakiltar jahar a majalisar dokoki ta kasa, suka ziyarci babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor, da kuma shugaban hafsoshin sojan kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru a Abuja.

Zulum, sanata Kashim Shettima (Borno ta Tsakiya), Mohammed Ali Ndume (Borno ta Kudu) da Abubakar Kyari (Borno ta Arewa), tare da shugaban rikon Borno na APC, Ali Dalori, sun gana da shugabannin ne kan hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai a wasu yankuna na jahar.

Dukkan ziyaran an yi su ne daban-daban kuma a cikin kowanne, an gudanar da tattaunawar ta sirri, Vanguard News ta ruwaito.

Dukkan ziyaran an yi su ne daban-daban kuma a cikin kowanne, an gudanar da tattaunawar ta sirri.

Kafin daya daga ciki, Zulum ya kai ziyarar gaisuwa a ofishin shugaban sojojin, yana mai godewa sojoji bisa kishin kasa, sadaukarwa da jajircewa a kokarin hada hannu don dawo da zaman lafiya a Borno.

Gwamnan duk da haka ya yi kira ga sojojin Najeriya da su ci gaba da inganta yarda tsakanin jama’a, gwamnati da sojoji.

“Dole ne muyi duk mai yuwuwa don inganta yarda tsakanin mutane, gwamnati, da sojoji. “Ya kamata mu hada kai, abu daya da ya kamata mu yi shi ne tabbatar da ayyukan da ake gudanarwa ya dore kuma manoma na iya komawa yankunansu na gona don mu rage dogaro da taimakon abinci wanda ba mai dorewa ba ne.

“Za mu bai wa sojoji dukkan goyon bayan da suke bukata, kuma za mu ci gaba da tattaunawa da ku, da fatan za a shawo kan wannan matsalar cikin kankanin lokaci ” in ji Zulum.

Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya yabawa gwamna Zulum bisa gagarumar goyon bayan da yake baiwa sojoji tare da bayyana ziyarar a zaman da ya dace.

Ya lura cewa irin wannan ziyarar tana ba da kofa don musayar ra’ayi mai amfani.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here