An Bude Ofishin NNPP na Jihar Borno Bayan Garkameshi da Kwana Daya
Bayan diramar da ya faru a jihar Borno ranar Alhamis, an bude sakatariyar jam’iyyar NNPP ta jihar.
Jam’iyyar ta NNPP ta zargi gwamnan jihar Babagana Zulum da alhakin kulle ofishin da kama shugabanta.
Shugaban APC na Borno, Ali Bukar Dalori ya musanta cewa jam’iyyarsu na da hannu kan lamarin, ya shawarci NNPP ta warware matsalarta da yan sandan.
Read Also:
Maiduguri – An bude ofishin jam’iyyar New Nigeria People Party NNPP na jihar Borno kwana daya bayan garkameshi da aka yi ranar Laraba.
Saifullahi Hassan, mai magana da yawun dan takarar shugaban kasa karkashin jam’yyar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da hakan a shafinsa na Tuwita.
Hassan yace bayan haka gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bada hakuri bisa abinda ya faru.
A cewarsa
“An bude Sakatariyar jam’iyyar @OfficialNNPPng da aka rufe jihar tare da bamu hakuri daga Gwamna.”
“Mun godewa yan Najeriya da suka tayamu caccakar wannan abin takaici da aka yi.”