Ranto Bashin Kudade: Shugaba Buhari ya Buƙaci Majalisa ta Bashi Damar

 

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya buƙaci majalisar dokokin ƙasar ta bashi dama ya ranto Naira 1,668, 417, 229, 124.5, wato Naira Triliyan daya da biliyan dari shida da sittin da takwas da miliyan dari hudu da goma sha bakwai da motsi.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa shugaban ya ce za a yi amfani da kudin ne domin aiwatar da kasafin kudin kasar na shekarar 2021.

Cikin wata wasika da shugaban ya aika wa majalisar dokokin kasar, ya ce bashin wani bangare ne na shirin yin rance, da aka tsara tun shekarar 2018 zuwa 2020.

Ya ƙara da cewa ciyo bashin ya zama dole, domin cimma burin aiwatar da wasu ayyuka da za su amfani jama’ar kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here