Shugaba Buhari ya Canza Ra’ayin Zama da ‘Yan Majalisa
Yan majalisa sun bukaci shugaban kasan ya yi musu bayanin dalilin da ya sa aka gaza shawo kan matsalar tsaro.
Bayan rikici da cece-kuce, Buhari ya amince zai bayyana gabansu kuma zai yi jawabi.
Bayan alkawarin gurfana gaban yan majalisan dokokin tarayya, Buhari ya canza ra’ayinsa.
Read Also:
Ya tabbata cewa shugaba Muhammadu Buhari ya fasa bayyana gaban yan majalisar dokokin tarayya ranar Alhamis domin jawabin kan tabarbarewan tsaro a fadin tarayya.
TVCNews ta samu bayani daga bakin mai tsawatarwa a majalisa, Muhammad Munguno cewa shugaban kasan ya canza ra’ayinsa.
Ya ce ana kyautata zaton Buhari ya canza ra’ayinsa na zuwa ne saboda zargin da ake cewa yan majalisan PDP za su ci mutucinsa.
Yan majalisan PDP sun yi ganawar sirri a daren Talata.