Shugaba Buhari ya Dawo Najeriya Bayan Kwanaki 16 a Birnin Landan

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira babban tashar jirgin kasa da kasa ta Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja daga birnin Landan bayan makonni biyu inda yaje ganin Likita.

Buhari ya dira Abuja ne misalin karfe 5 na yammacin Alhamis, 15 ga Afrilu 2021.

Mun kawo muku rahoton Jaridar Punch na ruwaito cewa komai ya kankama don dawowar shugaba Muhammadu Buhari yau.

Buhari ya tafi Landan tun ranar 30 ga Maris da sunan zuwa duba lafiyarsa kamar yadda ya saba. A cewar rahoton, an kammala shirye-shiryen tarban shugaban kasa kuma ana kyautata zaton dirarsa Abuja Najeriya yanzu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here