Shugaba Buhari Zai Gabatar da Kasafin Kudin 2023 ga ‘Yan Majalisar Tarayya

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatarwa ‘yan majalisar tarayyar kasar nan kasafin kudin shekarar 2023.

Kamar yadda shugaba majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya sanar, hakan zata faru ne a ranar Juma’a wurin karfe 10 na safe.

Shugaba Buhari zai mika kasafin N19.76 tiriliyan ga ‘yan majalisar a zauren wucin-gadi na majalisar wakilan Najeriya.

Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudi N19.76 tiriliyan na shekarar 2023 ga majalisar tarayyar kasar nan a ranar Juma’a.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a zaman majalisar na ranar Talata, yace shugaban kasar zai yi wannan gabatarwan da karfe 10 na safe a zauren majalisar wakilai na wucin-gadi.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here