Shugaba Muhammadu Buhari ya Shiga Ganawa da Shugabannin Tsaro na Najeriya a Fadar Shugaban Kasa

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaro ta kasa a fadar shugaban kasa.

Sai dai kuma zuwa yanzu babu wani cikakken bayani kan ajandar amma baya rasa nasaba da yanayin tsaron kasar.

Hakan na zuwa ne sama da awanni 24 bayan wasu barayi sun yi yunkurin kai hari gidan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.

A yanzu haka, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin ganawa da shugabannin tsaro na Najeriya a Fadar Shugaban kasa, Abuja.

Ganawar na zuwa ne sama da awanni 24 bayan wasu ‘yan fashi da makami sun yi yunkurin kai hari gidan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.

Fadar Shugaban kasar ta sanar da batun ganawar ne ta shafinta na Twitter amma ba ta bayar da cikakken bayani kan ajandar ta ba.

Taron wanda aka fara shi da karfe 10 na safe, ana yin sa ne a dakin taro na Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa.

Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da kuma mai bada shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Babban Lauyan kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyema; Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Salihi Magashi (Mai ritaya) da Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here