Shugaba Buhari ya Halarci Faretin Kaddamar da Sabbin Launuka na Rundunonin Sojan Najeriya

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci faretin kaddamar da sabbin launuka na rundunonin sojan Najeriya na 2023.

An gudanar da bikin kaddamarwan ne a dandalin Eagle da ke Abuja babban birnin ƙasar, inda shugaban ya samu rakiyar shugaban ma’aikata na fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari.

An ga shugaba Buhari sanye da kakin soja, inda yake zagayawa don duba sojoji sama da 1,000 da ke yin faretin.

Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor da Shugaban Rundunar Sojin Najeriya Laftanar-Janar Faruk Yahaya da Sufeton Ƴan Sanda Usman Alkali Baba na cikin mutanen da suka halarci bikin kaddamarwan.

Sauran waɗanda suka halarci bikin sun haɗa da Shugaban Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Oladayo Amao da Shugaban Rundunar Sojin Ruwa, Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo da kuma Shugagan Majalisar Dattawa Ahmad Lawan.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here