EFCC: Wata ƙungiyar ta Buƙaci Shugaba Buhari da ya ja Kunnan Hukumar

Wata ƙungiyar masu ɗauke da makamai a yankin Naija Delta, ta buƙaci shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta umartar jami’an hukumar EFCC su janye daga harabar gidan jagoransu Tompolo, sannan a bude masa asusunsa na banki.

Kungiyar mai suna 21st Century Youths of the Niger Delta and Agitators ta bayyana damuwa dangane da yadda aka ki mutunta umarnin wata kotu na wanke jagoran nata.

Cikin wata sanarwar Email da kungiyar ta fitar kamar yadda jaridar The Natiins ta rawaito, ta ce jan hankalin ya zama dole domin gudun haddasa danyar fitina a yankin na Naija Delta.

“A bawa Tompolo kadarorinsa da aka karbe, matasan kabilar Ijaw da kuma na Naija Delta ba za su sake naɗe kafa su tsaya suna kallon irin wannan cin fuska ba” ” ini sanarwar.

Kungiyar ta kara da cewa idan har aka gaza yin abinda ta nema, to kuwa za ta tura mutanenta su mamaye gidan da har ywnzu jami’an EFCC ke ci gaba da mamaya a cikinsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here