Shugaba Buhari na kaddamar da sababbin Kayayyakin Aikin Tsaro na ‘Yan Sanda

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, na kaddamar da sababbin kayayyakin aikin kwantar da tarzoma na rundunar ‘yan sandan kasar a hedikwatarta da ke Abuja a yau din nan.

Kayayyakin sun hada da motoci da makamai da kayayyakin sulke na jam’ian ‘yan sandan da kuma abubuwan kafa shinge da na tarwatsa masu zanga-zanga a lokacin tashin-tashina.

Rundunar ‘yan sandan na kaddamar da kayayyakin ne yayin da kasar ke tunkarar zabukanta na wannan shekara ta 2023, inda za a fara da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya ranar 25 ga watan nan na Fabarairu.

Sai kuma ranar 11 ga watan Maris lokacin da za a yi zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun dokoki na jihohi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here