Tsaro Aiki ne na Kowa, Kuma Shugaba Buhari ya yi Iyakar Kokarinsa Wajen Ganin bai Gaza Kare ‘Yan Kasarsa ba – Alhassan Doguwa

 

Dan majalisar wakilai na Najeriya ya bayyana irin kokarin da shugaba Buhari ya yi a fannin da ya shafi tsaro.

Alhassan Ado Doguwa ya karbi lambar yabo daga al’ummar jihar Kano a matsayin dan majalisar da ya ba da gudunmawa a harkar tsaro.

Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya na yawan fama da hare-haren ‘yan bindiga, musamman a shekarun baya-bayan nan.

Jihar Kano – Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya yaba da irin kokarin da shugaba Buhari ya yi na kare ‘yan Najeriya da dukiyoyinsu.

Doguwa ya dage cewa, tsaro aiki ne na kowa, kuma shugaba Buhari ya yi iyakar kokarinsa wajen ganin bai gaza kare ‘yan kasarsa ba.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi 22 ga watan Agusta a jihar Kano yayin wani aron karrama shi.

Rahoton jaridar TheCable ya ce, an karrama Doguwa ne a matsayin dan majalisar da ya saya sayin daka a fannin da ya shafi lamurran tsaro.

Kada ku daura laifi kan Buhari, tsaro aikin kowa ne Da yake karin haske game da matsalar da Najeriya ke ciki, jaridar Punch ta ruwaito Doguwa na cewa, bai kamata ‘yan Najeriya su daura laifin masalar tsaro ga shugaba Buhari kadai ba.

Ya kuma kalubalanci ‘yan kasar kowa ya kawo nasa gudunmawa wajen magance masalar tsaro, tare da cewa tunda kowa na alfahari da kasancewa dan Najeriya, to tsaro aiki ne na kowa. Hakazalika, ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar gwamnonin Najeriya su ci gaba da irin kokarin da suke na tallafawa baun tsaro.

A bangare guda, ya yabawa malamai a Najeriya bisa kokarin da suke a fannin lamarin tsaro, haka nan ga sarakunan gargajiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here