Shugaba Buhari ya yi Magana Kan Bude Boda

 

Babban Albishiri ga yan Najeriya, Buhari ya bayyana abinda ya tattauna da gwamnoni.

Ya zauna da su bayan zaman majalisar zartaswar jam’iyyar All Progressives Congress APC.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai bude iyakokin Najeriya.

Ya bayyana hakan ga gwamnonin Najeriya 36 a ganawar da yayi da su ranar Talata, 8 ga watan Disamba, 2020.

Buhari ya ce ya rufe iyakokin ne domin hana fasa kwabrin makamai da kwayoyi amma tun da yanzu makwabtan Najeriya sun hankalta, zai iya bude wa.

Buhari ya bayyana tattaunawarsa da gwamnonin a shafinsa na Tuwita.

“A ganawa da gwamnoni yau nayi bayanin cewa an kulle iyakokin Najeriya na kasa ne domin lura da fasa kwabrin makamai da kwayoyi. Amma yanzu da sakon ya isa ga kunnawan makwabtanmu, muna tunanin budewa nan ba da dadewa ba,” Buhari yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here