Buhari ya Umarci Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya yi Murabus: Emefiele ya yi Martani Kan Labarin

Gwamna Godwin Emefiele na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce yana jin dadin duk wani wasan kwaikwayon da ke zagaye da burinsa na takara a 2023, Daily Trust ta rawaito.

Emefiele ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wata ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja, ranar Alhamis.

Da aka tambaye shi game da martaninsa kan rahoton cewa shugaban kasar ya bukaci ya yi murabus bayan ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa na APC mai mulki, Emefiele ya ce:

“Babu labari a yanzu, amma za a samu labari a nan gaba. Kun ji ni, na ce ba labari yanzu amma za a samu labari nan kusa.”

Amma da aka bayyana masa cewa, ’yan Najeriya sun damu da matsayinsa, sai ya ce:

“Ku bar su su kamu da ciwon zuciya. Yana da kyau a kamu da ciwon zuciya. Ina jin dadi hakan sosai.”

Gwamnan babban bankin dai na fuskantar matsin lamba tun bayan da ya sayi fom din tsayawa takara na jam’iyyar APC mai mulki, lamarin da ya harzuka da dama inda wasu da dama ke kiransa da ya sauka daga mulki.

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya bayyana yadda ya ji kan batun takarar gwamnan CBN, inda ya roki Buhari ya kore shi idan ya ki sauka daga mukaminsa.

Sai dai a jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan faruwar lamarin, Emefiele ya ki amincewa da fom din shugaban kasa da aka saya masa, yana mai cewa zai yi amfani da dukiyarsa wajen siyan fom idan har yana sha’awar takarar.

Karin bayani na nan tafe…

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here