NNPC: Shugaba Buhari ya Nada Darektocin Hukumar Gudanarwar kamfanin

 

Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayinsa na Ministan harkokin man fetur ya bayar da umarnin mayar da kamfanin mai na NNPC a matsayin wanda zai iya ba da dama a zuba hannun jari, wato Nigerian National Petroleum Company Limited.

Wannan ya yi dai-dai da bangare na 53(1) na Dokar Man Fetur ta 2021, wadda ta bukaci Ministan Man Fetur ya mayar da kamfanin wanda za a iya zuba jari cikin wata shidda bayan sa hannu kan dokar.

Don haka ne Shugaba Buhari ya bukaci shugaban kamfanin, Malam Mele Kolo Kyari, ya dauki matakan da suka dace don tabbatar da sauya kamfanin.

Haka kuma, Shugaba Buhari ya nada darektocin hukumar gudanarwar kamfanin.

Sanata Ifeanyi Ararume shi ne ciyaman din hukumar gudanarwar kamfanin yayin da Mele Kolo Kyari ne shugaban hukumar sannan Umar I. Ajiya ne babban darektan da ke kula da harkokin kudi.

Sauran mabobin hukumar sun hada da Dokta Tajudeen Umar da Misis Lami O. Ahmed da Mallam Mohammed Lawal da Sanata Margaret Chuba Okadigbo da Barrister Constance Harry Marshal da Cif Pius Akinyelure.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here