Buhari: Mun Shawo Kan Matsalar Tsaro a Yankin Arewa Maso Yamma da Tsakiya

Ina matukar farin cikin yadda mulkina ya samar da tsaro da kwanciyar hankali a arewacin Najeriya, cewar Buhari.

A cewarsa,mulkinsa ya samar da tsaro a arewa maso yamma da tsakiyan arewacin Najeriya wanda ba’a samu ba tun 1960 – Ya fadi hakan ne a wata takarda da mai bashi shawara na musamman a harkar yada labarai, Femi Adesina, yasa hannu a ranar Laraba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mulkinsa ya kawo karshen rashin tsaro a arewa maso yamma da tsakiyan arewacin Najeriya.

A wata takarda da mai bashi shawara na musamman a kan harkar yada labarai, Femi Adesina ya saki a ranar Laraba, ya bayyana inda shugaba Buhari ya fadi hakan lokacin da ya ke kaddamar da ranar tunawa da sojoji ta 2021. Kamar yadda shugaban kasa yace, ana yin wannan taron ne don tunatar da ‘yan Najeriya yadda za su yi kishin kasa da kuma kawo hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya, wanda yayi wahala matuka kafin ya kai wannan matakin.

Buhari ya roki ‘yan Najeriya da su kiyaye yin abubuwan da za su kawo rabuwar kawuna tsakaninsu. Shugaban kasa ya kara da cewa, jami’an tsaro sun yi iyakar kokarinsu wurin kawo zaman lafiya arewa maso yamma da tsakiyan arewacin Najeriya.

Don yanzu haka arewa na cikin kwanciyar hankali. A cewarsa, “kasarmu ta fuskanci kalubale iri-iri a harkar tsaro tun da Najeriya ta samu ‘yancin kanta.

“Wadannan kalubalen ya jawo tattalin arzikin Najeriya, ilimi, harkokin lafiya da na noma sun yi kasa. “Ina farin cikin yadda aka samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso gabas da tsakiyan arewacin Najeriya.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here