Rabiu Kwankwaso: Shugaba Buhari ya Mika Sakon Ta’aziyyar Mahaifinsa

 

Allah ya yiwa mahaifin babban jagoran darikar Kwankwasiyya rasuwa.

An yi jana’izarsa bayan Sallar Juma’a a garin Kano.

Buhari ya siffanta marigayin matsayin mutum mai saukin sauki da tawali’u.

Shugaba Muhammadu Buhari ya jajantawa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa rasuwasr mahaifinsa, Alhaji Musa Saleh.

Shugaba Buhari, a sakon da ya aike ranar Juma’a yace Najeriya ta yi rashin daya daga cikin masu sarautar gargajiya dake da mutunci.

Buhari a sakon da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya saki, ya ce ba za’a iya mantawa da gudunmuwar da mahaifin Kwankwaso ya bada ba wajen hadin kan al’umma da zaman lafiya.

A cewar Buhari, “marigayi Salen mutum ne mai kyawun hali, mai tawali’u da saukin kai.

“Ina amfani da wannan damar wajen jajantawa tsohon gwamnan jihar Kano, gwamnatin jihar Kano, da masarautar Kano bisa mutuwar hakimin.”

“Allah ya yafe masa kura-kuransa kuma ya azurtashi da Aljannah, Amin,”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here