Taron Commonwealth 2022: Shugaba Buhari Zai Jagoranci Najeriya Zuwa Rwanda

Jirgin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai daga zuwa kasar Rwanda domin halartan taron shugabannin kungiyar Commonwealth na 2022.

Shugaba Buhari zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa wannan babban taron ne a cikin mako mai zuwa.

Stanislas Kamanzi, babban kwamishinan Rwanda a Najeriya ne ya bayyana hakan a wajen wani taro da aka gudanar a babbar birnin tarayya Abuja.

Abuja – Shugaban kasa Muhammadu zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron kasashe rainon Ingila wato Commonwealth na 2022 wanda aka shirya gudanarwa a Kigali, kasar Rwanda, a mako mai zuwa.

Stanislas Kamanzi, babban kwamishinan Rwanda a Najeriya ne ya bayyana hakan a wajen taron sada zumunta na kafin taron na CHOGM 22 da aka gudanar a Abuja, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya ce:

“Kasar Rwanda da mutanenta sun shirya karbar bakuncin daya daga cikin manyan tarukan duniya tare da manyan shugabanni da tawagoginsu da za su hallara.

“Abin farin ciki ne a gareni na mika godiya ga gwamnatin tarayyar Najeriya musamman ma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amsa gayyatar da shugaba Paul Kagame ya yi masa da kuma muhimmiyar tawagar da zai jagoranta zuwa Kigali.”

Kamanzi ya bayyana cewa taron zai zama wani dandalin muhawara da daukar matakai kan batutuwan na gama gari, wadanda suka hada da: shugabanci da bin doka; kiyayewa tare da alaka tsakanin tattalin arziki da muhalli; lafiya; fasaha da matasa.

Babban kwamishinar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta ce a yanzu Birtaniya a shirye take ta mika wa kasar Rwanda shugabar kungiyar Commonwealth bayan shekaru hudu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here